Saudiya

Mutane dubu 1 ne kacal za su yi aikin hajjin bana

Gwamnatin Saudiya ta ce, kimanin mutane dubu 1 ne kacal da ke zaune a cikin kasar za su gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus da ta tilasta rage yawan maniyata.

Masallacin Makka mai alfarma da ke Saudiya
Masallacin Makka mai alfarma da ke Saudiya STR / AFP
Talla

Ministan Kula da Aikin Hajji na kasar, Mohammad Benten ya sanar da haka ga manema labarai a birni Riyadh, yana mai cewa adadin mahajjatan na bana ka iya kasa da dubu 1.

Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin kasar ta bada tabbacin cewa, za a gudanar da aikin hajjin bana, amma ga mutanen da ke zaune a cikin kasar, ma’ana dai, ban da baki daga kasashen ketare.

Tuni al’ummar Musulmi daga sassan duniya suka fara mayar da martani, inda wasu ke bayyana rashin jin dadinsu da matakin hana dimbin Musulmai sauke farali a bana.

A kowacce shekara dai, ana samun a kalla Musulmai miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajji a kasar Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI