Amazon

Amazon zai zuba dala biliyan 2 don yaki da dumamar yanayi

Tun a bara ne kamfanin ya sha alwashin taka muhimmiyar rawa wajen yaki da gurbacewar yanayin don daidaituwa da bukatar yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris.
Tun a bara ne kamfanin ya sha alwashin taka muhimmiyar rawa wajen yaki da gurbacewar yanayin don daidaituwa da bukatar yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris. Flickr / Creative Commons

Kamfanin Amazon ya sha alwashin zuba jarin dala biliyan 2 ga bangarorin da za su taimaka wajen rage dumamar yanayi a wani mataki na rage yawan sinadaran hayaki mai guba da kamfanoni ke fitarwa don mara baya ga shirin kasashen duniya na yaki da gurbacewar yanayi.

Talla

Kamfanin na Amazon da ke sanar da matakin a jiya cikin sanarwar da ya fitar ya ce adadin kudin na dala biliyan 2 da za a zuba a bangarori daban-daban zai taimakawa kamfanonin cimma muradin kawo karshen fitar da hayaki mai guba ba kuma tare da hakan ya shafi tattalin arzikinsu ba.

Jagoran kamfanin na Amazon Jeff Bezos ya ce tsabar kudin zai taimaka wajen samar da sabbin fasahohi na zamani da da za su bunkasa tattalin arzikin kamfanoni tare da taka muhimmiyar rawa wajen dakile yawan sinadaran hayakin mai guba da kamfanonin ke fitarwa.

Sanarwar ta Amazon ta ce kamfanoni daga ilahirin sassan duniya kama daga masu tasowa zuwa wadanda suka bunkasa dole ne su aminta da shirin kawo karshen fitar da sinadaran hayaki mai gubar don ceto duniya daga barazanar da ta ke fuskanta na dumamar yanayi.

Matakin na Amazon dai na matsayin wani bangare na alkwarin da kamfanin ya yi a bara kan cewa zai rage yawan sinadaran hayakin mai gurbata muhalli da ma’aikatunsa ke fitarwa don yin dai dai da bukatar yarjejeniyar yanayi ta Paris da ke fatan kawo karshen fitar da nau’in sinadaran masu gurbata yanayi, yayinda kuma ya sha alwashin karfafa gwiwar sauran kamfanoni wajen ganin sun mara baya ga tsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.