Coronavirus

Coronavirus za ta harbi mutun miliyan 10 a makon gobe-WHO

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black / World Health Organization / AFP

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa, adadin masu dauke da cutar coronavirus zai kai miliyan 10 nan da makon gobe a sassan duniya, yayin da ta yi gargadin cewa, har yanzu cutar ba ta kai matakin kololuwa ba a kasashen yankin Amurka.

Talla

Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa wani taron kafar bidiyo cewa, a farkon watan da annobar coronavirus ta barke, kasa da mutane dubu 10 aka rawaito sun harbu da ita, amma a cikin watan jiya, kusan mutane miliyan hudu suka kamu da ita.

Ghebreyesus ya ce, a yanzu suna sa ran adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 10 nan da makon gobe.

Shugaban na WHO ya ce, wannan tunatarwa ce mai sosa rai duk da cewa, suna kan ci gaba da gudanar da bincike kan riga-kafin cutar da maganinta, amma akwai nauyin gaggawa da ya rataya a wuyansu don ganin sun yi amfani da kayayyakin da ke hannunsu a yanzu wajen dakile yaduwar cutar tare da ceto rayukan jama’a a cewarsa.

Sabuwar kwayar cutar ta coronavirus ta kashe mutane a kalla dubu 477 da 500, sannan ta harbi mutane miliyan 9 da dubu 300 tun bayan barkewarta a karshen shekarar bara a China.

Darektan Kula da Ayyukan Gaggawa na WHO Michel Ryan ya gargadi cewa, har yanzu wannan cuta na ragargazar kasashen yankin Amurka, yana mai cewa, akwai bukatar gwamnatoci su dauki tsauraran matakan rage bazuwarta.

Jami’in ya ce har yanzu, wannan cuta ta tsananta a kasashen yankin Amurka musamman a Tsakiya da Kudancin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI