Amurka-Isra'ila

Muna goyon bayan Isra'ila kan mamaye Falasdinu-Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Andrew Harnik/Pool via REUTERS

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce suna goyan bayan duk wani shiri da Isra'ila ke yi na mamaye yankunan Falasdinawa da zummar samarwa kanta tsaron da ya dace duk da sukar da kasashen duniya ke yi kan matakin.

Talla

Pompeo ya shaida wa manema labarai cewa, batun mamaye filayen, ‘yanci ne na Isra'ila kuma tana da hurumin yin haka, yayin da ya ce Amurka na magana da kasashen da ke Yankin Gabas ta Tsakiya kan yadda za su magance duk wata barakar da ka iya tasowa domin cimma burinsu.

Sakataren ya ce, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da shugabannin kasashen da ke Yankin Tekun Fasha duk sun amince da shirin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya da shugaba Donald Trump ya gabatar a watan Janairu, wanda ya bai wa Isra'ila goyan-bayan mamaye yankunan Falasdinawan.

Pompeo ya ce abin takaici ne yadda Kungiyar Falasdinu kadai a Yankin ta ki amincewa da shirin, inda yake cewa yana fatar ganin nan da makwanni masu zuwa, za su ci gaba da samun nasara kan shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI