Coronavirus

Masu coronavirus sun zarce miliyan 10

Coronavirus ta kashe mutane kusan dubu 500
Coronavirus ta kashe mutane kusan dubu 500 indiatimes

Sama da mutane miliyan 10 sun harbu da kwayar cutar coronavirus a sassan duniya kamar yadda alkaluman hukumomin kiwon lafiya suka suna, kuma nahiyar Turai da Amurka ke da rabin adadin masu dauke da annobar.

Talla

Adadin mutanen da wannan cuta ke kamawa ya rubanya tun a ranar 21 ga watan Mayu, inda a cikin kwanaki shida da suka shude ta harbi mutane miliyan 1.

Kawo yanzu wannan annoba ta lakume rayukan jama’a akalla dubu 498 da 779 tun daga lokacin da ta fara bulla a karshen shekarar bara a kasar China .

Sai dai masana kiwon lafiya sun gargadi cewa, hakikanin adadin mutanen da coronavirus ta harba ya zarce alkaluman da hukumomin lafiya na duniya ke bayarwa da kimanin ninki 10, lura da cewa, akwai dimbin wadanda suka kamu da ita, amma ba a yi musu gwaji ba a hukumance ko kuma suna dauke da cutar ba tare da nuna alamominta ba.

A nahiyar Turai kadai, cutar ta kashe mutane dubu 195 da 975, yayin da a Amurka ta aika dubu 125 da 539 lahira.

Brazil wadda ke matsayin kasa ta biyu a duniya da wannan cuta ta fi yi wa barna, ta yi asarar mutane sama da dubu 1 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata kadai.

Wannan adadi na miliyan 10 da aka samu na zuwa ne bayan kasashen da cutar ta fi kamari sun fara sassauta dokar hana fitar gida wadda aka kafa don hana bazuwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI