Coronavirus

Coronavirus ta lakume rayuka fiye da rabin miliyan

Adadin mutanen da coronavirus ta kashe ya zarta dubu 500 a sassan duniya.
Adadin mutanen da coronavirus ta kashe ya zarta dubu 500 a sassan duniya. REUTERS/Ueslei Marcelino

Sama da mutane dubu 500 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a sassan duniya, yayin da ta harbi fiye da miliyan 10, kuma nahiyar Turai da Amurka ke da rabin adadin masu dauke da annobar.

Talla

Adadin mutanen da wannan cuta ke kamawa ya rubanya tun a ranar 21 ga watan Mayu, inda a cikin kwanaki shida da suka shude ta harbi mutane miliyan 1.

Sai dai masana kiwon lafiya sun gargadi cewa, hakikanin adadin mutanen da coronavirus ta harba ya zarce alkaluman da hukumomin lafiya na duniya ke bayarwa da kimanin ninki 10, lura da cewa, akwai dimbin wadanda suka kamu da ita, amma ba a yi musu gwaji ba a hukumance ko kuma suna dauke da cutar ba tare da nuna alamominta ba.

A nahiyar Turai kadai, cutar ta kashe mutane dubu 195 da 975, yayin da a Amurka ta aika dubu 125 da 539 lahira.

Brazil wadda ke matsayin kasa ta biyu a duniya da wannan cuta ta fi yi wa barna, ta yi asarar mutane sama da dubu 1 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata kadai.

Wannan adadi na miliyan 10 da aka samu na zuwa ne bayan kasashen da cutar ta fi kamari sun fara sassauta dokar hana fitar gida wadda aka kafa don hana bazuwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI