Isra'ila

Mamaye yankin Falasdinawa tamkar shelanta yaki ne- Hamas

Kungiyar Hamas ta gargadi Isra'ila cewa, muddin ta kuskura ta fara aiwatar da shirin mamaye yankin Falasdinawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, tamkar ta shelanta yaki ne.

Falasdinawa na zanga-zangar adawa da shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar
Falasdinawa na zanga-zangar adawa da shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar Mohammed Salem/Reuters
Talla

Kafin kungiyar Hamas, Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasahsen Larabawa da ta Turai duk sun yi Allah-wadai da shirin Isra'ila na mamaye yankunan daga ranar 1 ga watan gobe, inda suka bayyana cewar matakin na iya haifar da tashin hankali da kuma hana shirin kafa kasar Falasdinu.

Mai magana da yawun kungiyar Hamas Abu Ubaida ya ce, suna tintibar wasu kungiyoyin da ke yankin domin daukar matsayin bai-daya wajen tunkarar Isra'ilar da zarar ta fara aiwatar da shirin.

A 'yan makwannin nan dai, kusan kowacce rana ake gudanar da zanga-zanga a yankin zirin Gaza da ke karkashin ikon Hamas don nuna adawa da shirin zaman lafiyar da shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar a yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI