Addini

"Masu mulkin mallaka ne suka kawo ta'addanci"

Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsalar ta'addanci a duniya
Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsalar ta'addanci a duniya News Ghana

Wani Shehin Malamin Kimiyar Siyasa a Jami’ar California da ke Santa Cruz a Amurka, ya bayyana tsarin mulkin mallaka a matsayin kashin-bayan tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci, yana mai cewa, kar a kuskura a dora laifin tsananin kishin Islama kan shari’ar Musulunci.

Talla

Makalar da Shehin Malamin Masanin Kimiyar Siyasar, Mark Fathi Massoud ya wallafa na zuwa ne a daidai lokacin da ake gargadin cewa, masu tsananin ra’ayin kishin Islama na son kafa tsauraran dokokin addini a Amurka, yayin da wasu ‘yan majalisun jihohin kasar suka yi yunkurin haramta Shari’ar Musulunci.

Sai dai a makalar tasa, Massoud ya mayar musu da martani, yana mai cewa, sun jahilci hakikanin ma’anar Shari’a wadda ya ce, ko kadan ba ta kunshi dokoki masu tsauri ba, hasali ma, tana nufin ‘hanya’ kuma an gina ta ne akan Alkur’ani da Sunnar Manzan Allah.

Malamin ya ce, bincikensa na tarihi, ya nuna cewa, shugabannin jira-jiran kasashen Musulmi da aka yi wa mulkin mallaka, sun zabi ci gaba da amfani da tsarin dokokin da Turawan Mulkin mallakar suka shinfida musu a maimakon su ci gaba da amfani da tsarin da aka san su akai na shari’ar Musulunci a tsakankanin shekarun 1950 zuwa 1960.

Sabbin kasashen da suka samu ‘yanci irinsu Najeriya da Pakistan da Somalia, sun ci gaba da aiwatar da tsarin Shari’a a fannin auratayya da rabon gado a wasu yankuna, amma sun dauki tsarin dokokin kasashen Turai a wasu bangarori.

A takaice dai, shehin malamin ya gano cewa, tsarin dokokin masu mulkin mallaka, shi ne ummul haba’isin rarrabuwar kawuna tsakanin addinai da kabilu musamman a kasar Sudan, lamarin da daga bisani ya haddasa ta’addanci.

Kazalika Farfesa Massoud ya ce, bincikensa ya nuna masa cewa, rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika sun samo asali ne daga matakin da masu mulkin mallaka suka dauka na yin watsi da tsarin Shari’ar Musulunci, yayin da kasashen Musulmi suka kankame wa tsarin na Turawa don samun yardarsu a cerwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.