Coronavirus

An cika watanni 6 da fara fuskantar annobar COVID-19 a duniya

Watanni 6 kenan kasashen duniya na ci gaba da daukar matakan kariya daga cutar wadda a kullum ke kara tsananta.
Watanni 6 kenan kasashen duniya na ci gaba da daukar matakan kariya daga cutar wadda a kullum ke kara tsananta. Jung Yeon-je / AFP

Dai dai lokacin da ake cika watanni 6 da bullar cutar coronavirus ko kuma COVID-19 a duniya, hukumar lafiya ta WHO ta yi gargadin cewa ko kadan ba a wuce annobar cutar coronavirus ba, domin kuwa a yanzu haka somin tabi aka fara gani na bannar da cutar za ta yiwa duniya.

Talla

Cikin bayanan da WHO ta fitar jiya, bayan cika watanni 6 da bullar cutar wadda a karon farko ta bayyana a yankin Wuhan na tsakiyar China, shugaban hukumar Tedros Adhanom, ya ce duk da matakan da kasashen duniya ke dauka na yaki da cutar a kowacce rana adadin masu kamuwa da ma wadanda ke mutuwa na sake karuwa, wanda ke nuna bannar da cutar za ta tafkawa duniya gabanin zuwa karshenta.

Tedros Adhanom a jawabin nasa, ya ce watanni 6 da suka gabata, babu wanda ya yi tunanin annobar cutar ta coronavirus da ta faro daga China za ta jefa duniya a halin tsaka mai wuya.

Acewar hukumar ta WHO yaki da coronavirus na bukatar hakuri tare da aiki tare, domin kuwa sai an hada hannu ne za a iya yaki da ita, yana mai cewa sai a nan gaba ne cutar za ta kai ganiyarta.

Ya zuwa lokacin da Tedros Adhanom ke gabatar da jawabin dai, fiye da mutum miliyan 10 da dubu dari 1 coronavirus ta kama a sassan duniya yayinda ta kashe mutum dubu 501 da 847 galibi a Amurka da Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI