Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi tsagaita wuta a ilahirin rikicin da kasashe ke yi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da bukatar tsagaita wuta a duk yankunan da ake fama da tashin hankali sakamakon annobar COVID-19 da take cigaba da lakume rayuka, bayan kwashe watanni 3 ana tattaunawa tsakanin kasashen dake kwamitin.

Talla

Kudirin da Kwamitin Sulhun ya amince da shi wanda kasashen Faransa da Tunisia suka gabatar, ya bukaci gaggauta kawo karshen duk wani tashin hankalin da ake samu a kasashen duniya.

Jakadan Tunisia a Majalisar Dinkin Duniya Kais Kabtani ya yaba da wannan cigaban da aka samu, wanda ya baiwa kwamitin a karon farko daukar matsayin bai daya tun bayan barkewar annobar, yayin da masana ke bayyana shakku ko matsayin Majalisar zai yi tasiri a yankunan da ake fama da tashin hankalin.

Matsayin Majalisar ya kuma bukaci bangarorin dake rikicin da su rungumi aikin jinkai akalla na kwanaki 90 domin samun damar kai dauki ga wadanda rikicin ya ritsa da su.

Sai dai wannan matsayi na kwamitin sulhu bai shafi yankunan da ake yaki da yan ta’adda ba, yayin da kuma yayi shiru kan Hukumar Lafiya ta Duniya wadda kasar Amurka ke zargi da goyan bayan China wajen boye rahotan barkewar annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.