Ronaldo na daf da kafa tarihi a Juventus
Cristiano Ronaldo ya taimakawa kungiyar sa ta Juventus dake rike da kambin gasar Serie A, lallasa Genoa da ci 3 -1, lamarin da ya baiwa kungiyar damar ci gaba da rike matsayin jan ragamar teburin da tazarar maki 4.
Wallafawa ranar:
A wasan na daren Talata, har sai da akaje hutun rabin laokci babu wanda ya ci wani, bayan dawowa da mintuna 5 ne dan wasan Juventus Paulo Dybala ya jefa kwallon farko.
Kafin daga bisa ni Ronalda shima ya zura kwallo, wanda shine na 24 a kakar bana, abin da ke nuna cewa kwallo daya kachal ya ragewa masa ya kafa tarihin dan wasan farko da zai ciwa Juventus kwallaye 25 tun a shekarar 1960, lokacin da Omar Sivori ya kafa wannan tarihi.
Yanzu haka Juventus na jan ragamar teburin Seria A da maki 72, Lazio ke biye mata da maki 68 bayan doke Torino da ci 2-0 a wasan nasu na Talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu