Aniyar Isra'ila kan mamaye karin yankunan Falasdinawa ya fusata 'yan majalisar Amurka
Wani kawancen ‘yan siyasa ciki har da ‘yan majalisun Amurka da kuma kungiyoyin Yahudawa, sun bukaci kasar ta janye taimakon sojin da take baiwa Isra’ila, domin tilasta mata janye aniyar mamaye karin yankunan Falasdinawa a gabar kogin Jordan.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka ‘yar majalisar wakilan Amurka daga birnin New York Alexandria Ocasio-Cortez ta dukufa wajen tattara sa hannun takwarorinta kan wasikar kira ga shugaba Donald Trump da ya gaggauta daukar matakin haramtawa Isra’ila aiwatar da shirin na cigaba da mamayar yankunan falasdinawa a yamma da kogin Jordan.
Kunshe cikin wasikar dai, matsayin ‘yan majalisar ne dake jaddada cewar ya zama dole Amurka ta mutunta alkawarin da ta dauka na tabbatar da wanzuwar kasashen Isra’ila da Falasdinawa a karkashin tsarin cikakken ‘yanci, mutuntawa da kuma dimokaradiya.
A bangaren fitattun ‘yan siyasar Amurka kuwa, tuni Sanata Barnie Sanders tsohon dan takarar shugabancin Amurka da takwarorinsa suka sa hannun kan wasikar adawa da aniyar Isra’ila kan mamaye yankunan na Falasdinawa.
Bayaga wasikar ‘yan majalisar Amurkan da kuma manyan ‘yan siyasa, akwai wasu karin wasikun 5 dauke da sa hannun sama da mutane dubu 3 da kungiyoyin Yahudawa mazauna Amurka suka rubuta kan adawa da aniyar Isra’ilar kan Falasdinawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu