Turkiya-Saudiya

An fara shari'ar kisan Khashoggi a Turkiya

Turkiya ta fara shari’ar wasu mutane 20 dukkaninsu ‘yan asalin kasar Saudiyya da ake zargi da hannu wajen kashe dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul.

Kasashen duniya sun kadu da mugun kisan da aka yi wa  Jamal Khashoggi
Kasashen duniya sun kadu da mugun kisan da aka yi wa Jamal Khashoggi Yasin AKGUL / AFP
Talla

Mutanen 20 cikinsu har da biyu na hannun daman Yerima Mohammed bin Salman, an fara yi masu shari’a a wannan Juma’a ne ta bayan idonsu, bisa zargin cewa su ne suka kashe Jamal Khasgoggi a shekara ta 2018.

Khashoggi dan asalin kasar ta Saudiyya mai shekaru 59, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya ziyarci ofishin jakadancin kasar da ke  domin samun wasu muhimman takardu daidai lokacin da yake shirin auren wata ‘yar Turkiyya mai suna Haitce Cengiz.

Masu shigar da kara a Turkiyya sun yi zargin cewa, mataimakin shugaban hukumar tara bayanan sirrin kasar Saudiyya Ahmed al-Assiri, da wani babban jami’i a fadar Sarkin Salman mai suna Saud al-Qahtani na da hannun a wannan kisa, bisa zargin cewa su ne suka bayar da umarnin hallaka dan jaridar.

Sauran mutanen 18 kuwa sun hada da Maher Mutreb da ke aiki da hukumar tara bayanan sirrin kasar, sai kuma Salah al-Tubaigy da Fahad al-Balawi dukkaninsu manyan jami’an tsaron kasar ta Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI