Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga Faransa, inda shugaba Emmanuel Macron ya nada sabon Fira Ministan bayan murabus din na da Edouard Philippe.
Sauran kashi-kashi
-
Mu Zagaya Duniya Bitar labaran mako: Janye tallafin mai a Najeriya Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ta wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu labaran da suka wakana a makon da muka yi bankwana da shi masamman batun janye tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tunubu ya sanar.03/06/2023 20:14
-
Mu Zagaya Duniya Bitar labaran mako: Kungiyar kasashen Afirka ta ci ka shekaru 60 da kafuwa Shirin 'Mu Zagaya Duniya' da ke waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a cikin maako mai wucewa tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya waiwayi bukin ciki shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashen Afirka, a Najeriya 'yan kasar sun bayyana abin da suke so sabuwar gwamnati mai kamawa ta yi musu.27/05/2023 20:22
-
Mu Zagaya Duniya Mutane 10 sun mutu a wani sabon rikici da ya barke a jihar Filato da ke Najeriya Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba, ya waiwayi muhimman abubuwan da suka faru a duniya a makon da ya gabata. Daga cikin akwai halin da ake ciki a jihar Filato, inda aka akalla mutane 100 suka rasa rayukansu sakamkon wani sabon rikici da ya barke, da kuma shugabannin kasashen Afirka shida da za su yi tattaki zuwa Rasha da Ukraine, domin sulhunta yakin da kasashen suka shafe sama da shekara 1 suna gwabzawa.20/05/2023 20:16
-
Mu Zagaya Duniya Rahoton MDD ya bankado kisan fararen hula da sojoji suka yi a Mali. Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya saba waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a cikin maako mai wucewa. Daga cikin abubuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon, akwai rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana cewar sojojin Mali tare da dakarun kasashen ketare da ke taimaka musu a yakin da suke yi da taa'addanci sun kashe daruruwan fararen hula a shekarar 2022. Zaloka, baangarorin da ke riki da juna a Sudan sun bada dama a shigo da kayayyakin agaji inda ake da bukata.13/05/2023 21:03
-
Mu Zagaya Duniya Yadda bikin ranar ma'aikata ta duniya ya gudana Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba a kowane mako ya duba manyan abubuwan da suka wakana ne a makon da ya gabata. Shirn ya duba yadda aka gudanar da bikin ranar ma'aikata ta duniya a wasu sassan duniya, sannan ya duba batun rikicin da ya baarke a ksar Sudan, da irin kokarin da kasashen duniya ke yi na warware shi tun bayan da ya tashi a ranar 15 ga watan Afrilu a tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daaukin gaggawa na musamman.06/05/2023 22:00