Isa ga babban shafi
Amurka

Kashi 99 na masu cutar corona a Amurka basa cikin barazana - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin shirin gabatar da jawabin zagayowar ranar samun 'yancin kai daga Birtaniya a 1776. 4/7/2020.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin shirin gabatar da jawabin zagayowar ranar samun 'yancin kai daga Birtaniya a 1776. 4/7/2020. REUTERS/Carlos Barria
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki wadanda suka gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen cin zarafin bakaken fata da wasu ‘yan sandan kasar ke yi.

Talla

Shugaban ya sha alwashin samun nasarar kan wadanda ya kira masu neman tada zaune tsaye a Amurka ne, yayin jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar a jiya asabar, 4 ga watan Yuli, yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar Birtaniya a shekarar 1776.

Yayin jawabin nasa, Trump ya kuma bayyana cewa, kashi 99 na wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Amurka, ba basa fuskantar barazana ga rayuwarsu.

Trump wanda a yanzu haka ke fuskantar suka kan matakan gwamnatinsa na yakar annobar coronavirus, ya nanata matsayinsa kan cewar tilas a hukunta China bisa sakacin da ta yi na rashin dakile annobar, abinda ya kai ga fantsamar ta zuwa kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.