Amurka-Iran

Bincike ya gano kuskuren da Amurka ta tafka a kisan Qasim Soleimani na Iran

Babbar jami'ar da ke bincike kan kisan gilla ta Majalisar Dinkin Duniya Agnes Calamard ta bayyana kisan da Amurka ta yiwa babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qasem Soleimani ta hanyar amfani da jirgi marar matuki a matsayin kisan da ya saba ka'ida.

Hoton babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qassem Soleimani da Amurka ta yiwa kisan gilla.
Hoton babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qassem Soleimani da Amurka ta yiwa kisan gilla. REUTERS/Naif Rahma
Talla

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniyar ta musamman mai kawo rahoto kan kisan gilla da wuce makadi da rawa wajen aiwatar da hukunci Agnes Callamard, ta ce kisan Janar Qasem Soleimani kwamandan Sojin na Iran abu ne da ya yi hannun riga da doka da kuma muradun majalisar, tana mai cewa babu wata kwakwarar shaidar da Amurka ta bayar, da ke nuni da cewa akwai shirin kai mata hari.

Sai dai wannan kwararriya ba ta na magana ne da yawun Majalisar Dinkin Duniyar ba ne illa gabatar da rahoton abin da ta gano a binciken da ta gudanar.

Za a gabatar da rahoton na ta a kan kisa ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuki mai shake da makamai, wanda ya mayar da hankali a kan kisan Soleimani a taron hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a Geneva ranar Alhamis mai zuwa.

A ranar 3 ga watan Janairu ne shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin kisan Janar Soleimani da jirgin sama mara matuki a kusa da filin tashi da saukan jiragen sama na birnin Bagadaza, yana mai bayyana hafsan sojin a matsayin kasurgumin dan ta’adda da ya dace a kawar daga doron kasa.

Harin Amurkan ya kuma rutsa da kwamandan sojin Iraki Abu Mahdi al-Muhandis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI