Coronavirus-WHO-AID

Corona ta kawo cikas a yaki da AIDS - WHO

Ma'aikacin jinya na daukan samfurin jini don gwajin cutar HIV.
Ma'aikacin jinya na daukan samfurin jini don gwajin cutar HIV. REUTERS/Dinuka Liyanawatte

Kasashen duniya 73 sun yi korafin cewa suna fuskantar barazanar karewar maganin rage radadin kwayar cutar Kanjamau sakamakon zuwan annobar coronavirus kamar yadda binciken Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya gano.

Talla

Binciken da Hukumar Lafiyar ta WHO ta gudanar na zuwa ne gabanin taron kasa da kasa da ake gudanarwa bayan shekara-biyu-biyu kan cutar Kanjamau, inda kasashen duniya 24 suka rawaito cewa ko dai suna da matukar karancin maganin rage radadin Kanjamau din ko kuma suna fuskantar katsewar ci gaba da shigo musu da shi.

Binciken na WHO na zuwa ne bayan wani zaman nazari da ta shirya a cikin watan Mayu tare da Hukumar Yaki da Kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, UNAIDS, inda suka yi hasashen cewa, katse rarraba maganin rage radadin na HIV a tsawon wata shida, ka iya ninka adadin mutanen da ke mutuwa a sanadiyar cutuka masu nasaba da Kanjamau a yankin Afrika da ke Kudu da Sahara a kadai.

A shekarar 2019, an kiyasta cewa, mutane miliyan 8 da dubu 300 ke amfana da maganin rage radadin a kasashen duniya 24, amma a halin yanzu wadannan kasashen na fuskantar karancin maganin.

Wannan adadin na mutane miliyan 8 da 300 na a matsayin kashi 33 na daukacin mutanen da ke amfana da irin wannan maganin a duniya baki daya.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, sakamakon bincikensu na da tayar da hankali.

Kawo yanzu babu maganin warkar da cutar Kanjamau, amma maganin ARV na taka muhimmiyar rawa wajen rage radadinta da kuma hana yaduwarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.