Amurka

Amurka ta fara janyewa daga WHO

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara janye kasar daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya bayan ya zarge ta da gazawa wajen yaki da annobar coronavirus da kuma daukar China a matsayin 'yar lele.

Shugaban Amurka Donald Trump na zargin WHO da nuna son kai wajen yaki da annobar coronavirus
Shugaban Amurka Donald Trump na zargin WHO da nuna son kai wajen yaki da annobar coronavirus Carlos Barria/Reuters
Talla

Amurka ita ce kasa mafi girma wadda ta fi bada gudunmawar kudade ga Hukumar Lafiyar wadda ke jagorantar yaki da cutukan da ke addabar duniya da suka hada da cutar shan-inna da kyanda da matsalar tabin hankali.

Hukumar ta WHO na ci gaba da shiga gonar Trump a daidai lokacin da masu dauke da cutar coronavirus ke karuwa, kuma tun da farko shugaban na Amurka ya yi barazanar dakatar da Dala miliyan 400 da kasarsa ke bai wa hukumar a duk shekara a matsayin gudunmawa.

Yanzu haka shugaba Trump ya sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a hukumance cewa, ya fara janye kasar daga WHO kamar yadda kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya sanar.

Janyewar za ta kankama gadan-gadan cikin shekara guda, wato nan da ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2021.

Sai dai Joe Biden da ake kyautata zaton zai fafata da Trump a zaben watan Nuwamba mai zuwa, ya ce zai dakatar da ficewar Amurka daga hukumar muddin ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI