Amurka

Limaman addini sun gargadi Trump kan hukuncin kisa

Sama da limaman addini dubu 1 suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na maido da hukuncin kisa kan masu miyagun laifuka bayan an dakatar da hukuncin shekaru 17 da suka gabata.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai maido da hukuncin kashe masu miyagun laifuka bayan an dakatar da shi
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai maido da hukuncin kashe masu miyagun laifuka bayan an dakatar da shi REUTERS/Carlos Barria
Talla

A cikin wata sanarwa da suka fitar, limaman addinin masu mabanbanta akidar Kirista, sun ce ya kamata a yanzu a mayar da hankali kan kare rayuka a daidai wannan lokacin da Amurka ke fama da coronavirus da matsalar tattalin arziki da kuma matsalar nuna wariyar launi a tsarin shari’ar kasar.

A watan jiya ne, Ma’aikatar Shari’ar kasar ta sanar cewa, gwamnatin tarayya za ta dawo da tsarin kashe masu miyagun laifukan a ranar 13 ga watan nan na Yuli.

Tun lokacin da aka maido da wannan tsarin kisan a shekarar 1988, mutane uku kacal aka aiwatar musu da hukuncin kisan.

Daga cikin jagororin addinin da suka rattaba hannu kan wasikar gargadin Trump da Ministsn Shari’a Bill Barr, har da shugabannin Cocin Katolika masu adawa da kisan da kuma mabiya akidar Evangelica da suka fi samun rarrabuwar kawuna kan lamarin.

Carlos Malave, shugaban Kungiyar Hadin Kan Majami’un Kiristoci ya ce, a matsayinsa na mabiyin akidar Evangelica, ya kadu da matakin da Amurka ta dauka na maido da kisan ‘yan kasarta, yana mai cewa, ya kamata a nesantar da tunanin maido da kisan a daidai wannan lokaci na annobar coronavirus.

Wata babbar Kotun Amurka ta yi watsi da karar da aka shigar mata da ke kalubalantar amfani da allura mai guba wajen kisan da za a yi wa Daniel Lewis Lee a ranar 13 ga watan nan na Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI