Najeriya-China

Lauyoyin Najeriya na neman diyyar coronavirus daga China

China ta yi watsi da bukatar wasu lauyoyin Najeriya da ke son gwamnatin Beijing ta  biya Najeriyar Dala biliyan 200 saboda asarar da kasar ta yi a dalilin annobar COVID-19, cutar da ake zargin cewa, an kirkire ta ne a Cibiyar Binciken Wuhan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na China, Xi Jinping
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na China, Xi Jinping Reuters/Kenzaburo Fukuhara
Talla

Ofishin Jakadancin China da ke Najeriya ya ce bukatar lauyoyin ba shi da tasiri a dokokin duniya, domin kuwa cutar ta yi wa duniya ba-zata, kuma ita kanta China kamar kowacce kasa ta fuskanci ukubar annobar.

Lauyoyin 11 sun bukaci kotu da ta tilasta wa gwamnatin China biyan wadannan kudade da suka bayyana a matsayin diyyar asarar da aka samu wajen rasa rayuka da tabarbarewar tattalin arziki da wahalar da 'yan kasar suka shiga da kuma hana harkokin yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI