Red Cross

Matsalar sauyin yanayi ta fi tasiri a kasashen da ake yaki

Kungiyar Agaji ta Kasa da Kasa Red Cross ta ce, matsalolin sauyin yanayi sun fi tasiri a kasashe masu fama da yake-yake da sauran nau’ukan tashe-tashen hankula.

Kasashen duniya na fafutukar yaki da dumamar yanayi
Kasashen duniya na fafutukar yaki da dumamar yanayi GREG BAKER / AFP
Talla

Cikin sabon rahoton da ta fitar, kungiyar  ta ce, manyan matsalolin yake-yaken da tashe-tashen hankulan sun rusa ayyukan noma da haddasa barkewar cutuka da kuma tilasta wa dubban mutane barin gidajensu.

Red Cross ta ce, ta gina rahoton nata mai taken “Idan ruwan sama ya koma kura” ne bisa gudanar da bincike a kudancin kasar Iraqi da arewacin Mali da kuma sassan kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, inda kwararrunta suka yi nazari kan yadda mutane ke fama da matsalolin yaki da sauyin yanayi da hanyoyin tunkarar kalubalen da kuma yadda suke aiwatar da matakan kariyar.

Red Cross ta ce, a halin da ake ciki mafi akasarin kasashe 20 da suka fi fama da matsalolin sauyin yanayi da gurbatar muhalli, na cikin hali na yaki, inda ta yi gargadin cewa, idan ba a dauki mataki ba, nan da shekarar 2050, akalla mutane miliyan 200 za su fada tsananin bukatar agajin gaggawa a duk shekara.

Binciken Kungiyar Agajin ya rawaito mutane a yankunan Mali da Iraqi na cewar gurbatar yanayi ya jefa su cikin matsalolin karancin ruwan sha da abinci, yayin da a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya rikicin manoma da makiyaya ya fi kamari, wanda tasirin sauyin yanayi ta taka muhimmiyar rawa akai.

A Iraqi kuwa, alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa, a tsakanin shekarun 1950 to 1990, mahaukaciyar guguwa mai dauke da rairayi da a turance ake kira da “sand storm na aukuwa ne sau 25 ko kasa da haka duk shekara, to amma kama daga 2013, guguwar rairayin na afkawa yankunan kasar sau akalla 300 a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI