Amurka

Trump zai hana biza ga daliban da ke karatu ta Intanet a Jami'o'in Amurka

Jami’o’in Harvard da MIT sun bukaci kotu da ta dakatar da umarnin shugaban Amurka Donald Trump da ke barazana ga Bizar dalibai ‘yan asalin kasashen waje da ke karatu a kasar, wadanda kuma ke daukar darussa ta kafar intanet saboda coronavirus.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump MANDEL NGAN / AFP
Talla

Jami’o’in sun mayar da martani ne kan sanarwar da hukumar shige da fice ta Amurka ta fitar da ke cewa, dole ne daliban su fice daga kasar ko kuma a mayar da su makarantun da ke bada darasin keke da keke.

Shugaban Jami’ar Harvard, Lawrence Bacow ya ce, za su yi tsayin daka kan wannan batu don ganin cewa, dalibansu ‘yan asalin kasashen ketare sun ci gaba da karatu ba tare da fuskantar barazanar maida su gida ba.

Shi dai shugaba Donald Trump na matsin lamba don ganin jami’o’i da makarantu sun koma azuzuwa nan da watan Satumba duk da cewa, ana ci gaba da samun dimbin masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar.

Hukumar shige da ficen Amurka ta ce, ma’aikatar harkokin wajen kasar ba za ta bada Biza ga daliban da suka yi rajistan daukar cikakkun darussa ta yanar gizo ba, sannan kuma ba za a lamunce musu shiga cikin kasar ba.

Ana kallon wannan matakin a matsayin yunkurin gwamnatin fadar White House wajen matsin lamba kan manyan makarantun Amurka da ke kaffa-kaffar komawa azuzuwa a daidai wannan lokacin da ake fama da annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI