Duniya-Coronavirus

Yawan masu cutar corona a duniya yayi hauhawar da ba a taba gani ba

Alkalumman hukumomin lafiya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara, sun nuna cewar annobar coronavirus da ta halaka sama da mutane dubu 565 daga cikin kusan miliyan 13 da suka kamu, na dada yin karfi a maimakon sauki, tun bayan shiga watan Yuli da muke ciki.

Wani yankin Wales a kasar Birtaniya bayan sassauta dokokin hana zirga-zirga don yakar annobar coronavirus. 11/7/2020.
Wani yankin Wales a kasar Birtaniya bayan sassauta dokokin hana zirga-zirga don yakar annobar coronavirus. 11/7/2020. Reuters
Talla

Sabon rahoton yace karin yawan wadanda suka kamu da cutar corona mafi yawa a duniya da aka samu cikin watan na Yuli, sun hada da na ranakun asabar da ta gabata da adadin sama da mutane dubu 230, a ranar Juma’a aka samu karin sama da mutane dubu 225, sai kuma Alhamis da a fadin duniya karin sama da dubu 220 suka kamu da cutar ta coronavirus.

Rahoton na AFP yace a jumlace daga 1 ga Yuli nan zuwa yanzu 12 ga watan kusan karin mutane miliyan 2 da rabi suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya, adadi mafi yawa cikin kankanin lokaci da aka gani tun bayan bullar annobar daga China a Disambar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI