China-Amurka

China ta laftawa 'yan majalisar Amurka takunkumi

Gwamnatin China ta kakaba takunkuman haramtawa wasu daga cikin shugabannin majalisar dokokin Amurka guda 3, gami da wani jakadan kasar shiga cikinta.

Tutocin kasashen China da Amurka.
Tutocin kasashen China da Amurka. AFP/FRED DUFOUR
Talla

Matakin na China dai ya nuna yadda dangantaka ta kara yin tsami tsakaninta da Amurka, kan tuhumar ta da cin zarafi musulmin kabilar Uighur a Xinjiang.

‘Yan majalisar dattijan Amurkan da China ta laftawa takunkumin sun hada da Sanata Marco Rubio, Ted Cruz da kuma Chris Smith, sai kuma jakadan Amurka mai sa ido kan ‘yan cin addini Sam Brownback, wadanda suka yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Chinar.

Matakin na China dai martani kan makamancinsa da Amurka ta dauka a ‘yan kwanakin da suka gabata, inda ta haramtawa kusoshin gwamnatin China takardar Biza, cikinsu harda shugaban jam’iyyar kwaminisancin China na yankin Xinjiang Chen Quangou da ake zargi da zama kashin bayan cin zarafin kabilu marasa rinjaye a yankin musamman Musulmi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun jima suna tuhumar China da cin zarafin Musulmi akalla miliyan 1 ‘yan kabilar Uighur da Turkic a yankin Xinjiang ta hanyar killace su da kuma tilasta musu barin addinin.

Dangantakar China da Amurka ta yi tsami ne kan batutuwa da dama da suka hada da kasuwanci, zargin sakaci kan annobar coronavirus, dokar tsaro kan Hong Kong da kuma manufofin China a yankunan Tibet da Xinjiang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI