Coronavirus

Sabbin mutane miliyan 71 za su shiga kangin talauci-MDD

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya kiyasta cewa, karin mutane akalla miliyan 71 za su fada kangin talauci a duniya saboda illar annobar coronavirus.

Coronavirus ta jefa mutane da dama cikin kangin rayuwa
Coronavirus ta jefa mutane da dama cikin kangin rayuwa Abdirazak Hussein FARAH / AFP
Talla

Sashin lura da tattalin arziki da walwalar rayuwa na Majalisar Dinkin Duniya ne ya yi hasashen tagayyarar akalla mutane miliyan 71, a dalilin annobar.

Rahoton ya ce, lamarin zai fi muni a kudancin nahiyar Asiya da kuma yankin Afrika da ke Kudu da Sahara, inda ake sa ran za su samu karin mutane miliyan 32 da kuma miliyan 26 da za su fada kangin talaucin.

Sahin lura da tattalin arzikin na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce, jami’ansa sun tattara rahoton binciken tare da hadin gwiwar tawagar kwararru sama da 200 daga hukumomin kasa da kasa sama da 40.

Kafin barkewar annobar coronavirus, wani rahoto da kwararru suka wallafa, ya yi hasashen cewar, kashi 6 cikin 100 na yawan al’ummar duniya za su ci gaba da rayuwa cikin tsananin talauci nan da shekarar 2030.

Karo na farko kenan da aka samu kiyasin karuwar adadin masu fama da talauci a duniya mai yawa tun bayan na shekarun 1998 da kuma 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI