Amurka

Alkalin Amurka ya dakatar da shirin Trump na dawo da dokar kisa a kasar

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AP Photo/Evan Vucci

Wani Alkali a Amurka ya bayar da umarnin dakatar da komawa aiwatar da hukuncin kisa da gwamnatin shugaba Donald Trump ke kokarin dawo da shi bayan dakatar da dokar shekaru 17 da suka gabata har zuwa wani lokaci nan gaba.

Talla

Kafin umurnin na sa an shirya aiwatar da hukuncin ne kan Daniel Lewis Lee mai shekaru 47, kuma tsohon dan kungiyar fararen fata zalla da aka samu da laifin kashe wasu iyalan gida daya su 3 a shekarar 1996.

Alkali Tanya Chutkan ya bada umurnin dakatar da kisan har sai an kamala shari’ar da ake yi kan irin maganin allurar da za’ayi masa ta kisa da wa suke kalubalanta a kotu.

Ko a farkon watan nan sai da fiye da limaman addini dubu 1 a Amurkan suka bukaci shugaba Donald Trump ya yi watsi da shirinsa na maido da hukuncin kisa kan masu miyagun laifuka bayan an dakatar da hukuncin shekaru 17 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.