Majalisar Dinkin Duniya

Mutum miliyan 690 za su fuskanci tsananin yunwa a duniya- MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa duk 1 cikin kowanne mutum 9 zai yi fama da matsananciyar yunwa a shekarar nan sakamakon yadda annobar coronavirus ta kassara harkokin samar da abinci a sassan duniya.

Agajin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.
Agajin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya. AFP Photo/Essa Ahmed
Talla

Cikin rahoton shekara shekara da sashen tabbatar da wadatuwar abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ke fitarwa, ya bayyana lamurra masu alaka da sauyi ko dumamar yanayi baya ga annobar coronavirus a matsayin abubuwan da suka ta'azzara karancin abinci mai gina jiki da ya kara yawan mutane masu fama da cutar kiba marar iyaka ciki har da kananan yra.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin mutum miliyan 690 dai dai da kashi 8.9 na yawan al’ummar duniya yanzu haka na fama da matsananciyar yunwa, alkaluman da suka dara jumullar mutanen da suka fuskanci yunwar a bara da yawan mutum miliyan 10 haka kuma karin mutum miliyan 60 idan an kwatanta da yawan mutanen da ke fadawa yunwa a shekarun baya.

Rahoton Majalisar ya nuna cewa abu ne mai wuya hukumar samar da abinci ta duniya ta iya cimma muradun yaki da yunwa da ake fata a shekarar 2050.

Rahoton ya ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, adadin mutanen da za su fada halin yunwar zai karu zuwa mutum miliyan 890 nan da shekarra 2030.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI