Gwamnan da ya halarci taron Trump na dauke da korona
Gwamnan jihar Oklahoma ya kamu da cutar coronavirus bayan ‘yan makwanni da halartarsa yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a jihar.
Wallafawa ranar:
Adadin masu dauke da cutar na karuwa a Oklahoma, yayin da hukumomin kiwon lafiya suka bayyana cewa, yakin neman zaben Trump da kuma zanga-zanzgar da aka gudanar a cikin watan Yuni, sun taimaka wajen tsanantar yaduwar cutar a jihar.
Gwamna Kevin Stitt ya yi amanna cewa, shi ne gwamna na farko a Amurka da ya kamu da coronavirus amma watakila ba a dandalin yakin neman zaben Trump ya dauki cutar ba.
Gwamnan mai shekaru 47 kuma dan jam’iyyar Republican ya ce, ya killace kansa daga iyalansa, sannan kuma zai ci gaba da gudanar da aiki daga gida har sai ya warke.
Gwamnan dai na yawan kin sanya kyallen rufe baki da hanci a taruka daban daban, kazalika bai sanya takunkumin ba a taron yakin neman zaben na Trump wanda ya gudana a ranar 20 ga watan jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu