Yawan al'ummar Duniya zai zarce biliyan 8 a shekarar 2100

Wani Binciken Majalisar Dinkin Duniya ya ce nan da shekarar 2100 za a samu karin mutane biliyan biyu a duniya abinda zai kawo adadin mutanen da ke doran kasa zuwa biliyan 8 da miliyan 800.

Taswirar Nahiyoyin Duniya.
Taswirar Nahiyoyin Duniya. Nations Online Project
Talla

Rahotan da aka wallafa shi yau a Jaridar The Lancet yace nan zuwa karshen wannan karnin, kasahse 183 daga cikin 195 zasu gaza wajen cigaba da daidaita yawan jama’ar dake cikin su.

Majalisar ta ce sama da kasashe 20 irin su Japan da Spain da Italia da Thailand da Portugal da Korea ta kudu da kuma Poland za su yi asarar rabin al’ummar su, kamar yadda China za ta gamu da raguwar jama’ar da ke kasar daga biliyan guda da miliyan 400 da ta ke da shi yanzu zuwa miliyan 730 nan da shekaru 80 masu zuwa.

Sai dai rahotan ya ce yawan jama’ar da ke Yankin kudu da saharar Afirka zai ribanya har sau uku zuwa biliyan 3, inda Najeriya kawai za ta samu yawan mutanen da zai kai miliyan 800 nan da shekarar 2100, inda za ta zama kasa ta biyu a duniya da tafi yawan jama’a bayan India mai mutane biliyan guda da miliyan 100.

Christopher Murray, Daraktan Cibiyar kula da lafiyar da ke Jami’ar Washington da ya jagorancin masana wajen gudanar da binciken ya ce binciken na su ya nuna cewar za a samu muhalli mai kyau da kuma samar da abincin da zai wadaci jama’a da raguwar gurbata muhalli, kana da karuwar harkokin tattalin arziki a yankin Afirka da ke kudu da sahara, yayinda kasashen da ke wajen Afirka za su gamu da matsalar ma’aikata abinda zai shafi tattalin arzikin su.

Rahotan ya ce nan da shekaru 80 masu zuwa ‘yancin mata zai samu gurbi a karkashin kowacce gwamnati, yayinda za’a bukaci inganta harkokin kula da lafiya da kuma jin dadin rayuwarsu domin inganta rayuwa.

Binciken ya ce yayin da za a samu raguwar haihuwa a fadin duniya, yawan yara ‘yan kasa ad shekaru 5 zai ragu da kashi 40, daga miliyan 681 da ake da shi a shekarar 2017 zuwa miliyan 401 a shekarar 2100.

Rahotan ya ce a wancan lokaci mutane biliyan 2 da miliyan 370 za su kasance suna da shekaru sama da 65, sama da kashi daya bisa 4 na jama’ar duniya, yayin da masu shekaru 80 za su karu daga miliyan 140 ayau zuwa miliyan 866.

Wannan bincike ya ce yawan mutanen da ke shekarun yin aiki a China zai ragu daga miliyan 950 ayau zuwa miliyan 350 a karshen wannan karnin, ita kuwa India wadda za ta fi yawan jama’a a lokacin za ta samu raguwar masu aikin yi daga miliyan 762 zuwa 578, yayin da Najeriya zata samu Karin yawan ma’aikata daga miliyan 86 ayau zuwa miliyan 578.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI