Rasha-Coronavirus

Rasha ta yiwa cibiyoyin binciken riga-kafin coronavirus kutse- Birtaniya

Hukumomin tsaro sun gargadi cewa, masu leken asiri daga Rasha na far wa cibiyoyi da kamfanonin da ke kokarin samar da riga-kafin annobar coronavirus a kasashen Birtaniya da Amurka da kuma Canada.

Kwararru sun dukufa wajen samar da riga-kafin cutar coronavirus
Kwararru sun dukufa wajen samar da riga-kafin cutar coronavirus Arnd Wiegmann/Reuters
Talla

Hukumar Tsaron Hanyoyin Sadarwar Intanet ta Birtaniya NCSC ta ce, lallai masu kutsen na aiki ne a wani bangare na Hukumar Leken Asirin Rasha, amma ba ta yi cikakken bayani kan cibiyoyi da kamfanonin da ake kokarin kai wa farmakin sace bayanansu ba.

Sai dai Hukumar ta NCSC ta ce, masu kutsen ba su yi nasarar dakatar da binciken da ake gudanarwa kan riga-kafin cutar coronavirus ba.

Tuni dai Rasha ta musanta wannan zargi, inda mai magana da yawun fadar gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov ya ce, ba su da bayanai game da duk wani mai kutse kan kamfanonin samar da magunguna da cibiyoyin bincike a Birtaniya, yana mai cewa abin da zai iya fadi shi ne, Rasha ba ta da hannu a wannan al’amari.

Hukumomin tsaro a Birtaniya da Canada da Amurka sun ce, masu leken asirin sun yi amfani da wata dama ta tangardar na’ura domin samun saukin kutsawa cikin rumbunan manyan kwamfutoci, inda suka yi amfani da shu’umar manhajar Malware wajen kwashe bayanai daga kwamfutocin da suka samu matsala.

Sai dai wasu masana na cewa, ga alama ba Rashawa kadai ba ne suka kaddamar da wannan kutse domin kuwa sun samu agaji daga wasu mutane daga Amurka da China kamar yadda Farfesa Ross Anderson na jami’ar Cambridge ya ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI