An kusan samun maganin coronavirus
Gwaje-gwajen da aka gudanar sun nuna cewa, wasu nau’uka biyu na riga-kafin coronavirus ba su da illa ga bil’adama, kuma suna samar da garkuwar jiki mai karfi ga masu dauke da cutar.
Wallafawa ranar:
Gwajin farko da aka gudanar a tsakanin mutane dubu guda masu yawan shekaru a Birtaniya, ya nuna cewa, riga-kafin ya haifar da karfafffiyar garkuwar jiki mai bada kariya daga cutar coronavirus.
Gwaji na biyu da aka gudanar a China kan mutane 500 ya nuna cewa, akasarin masu fama da cutar sun samu garkuwar jiki mai yaki da kwayoyin cuta.
Wannan bincike wanda aka wallafa a Mujallar Lafiya ta ‘The Lancet’, na a matsayin gagarumin ci gaba dangane da lalubo riga-kafin COVID-19 mai inganci kuma mara hadari ga al’umma.
Kodayake mawallafa binciken sun ce, sun gamu da ‘yar tangarda dangane da amfani da riga-kafin, suna masu gargadin cewa, akwai bukatar gudanar da karin bincike musamman kan dattawa masu yawan shekaru.
Daya daga cikin mawallafan Sarah Gilbert ta Jami’ar Oxford ta ce, sakamakon binciken na tattare da samun nasara kuma ana iya samar da wani adadi mai yawa na riga-kafin.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 600 a sassan duniya, yayin da ta kassara tattalin arzikin kasashen duniya tun bayan bullarta watanni bakwai da suka shude.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu