Amurka

Trump ya gargadi Amurkawa kan hadarin zaben Biden a watan Nuwamba

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Joe Biden, dan takarar da ake sa ran zai fafata da shi zaben watan Nuwamba, yana mai cewa, ba shi da kwarewar shugabancin kasar.

Talla

Shugaba Trump ya bayyana haka a yayin wata hira da kafar Fox News a dai dai lokacin da kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da zaben ta nuna cewa, masu kada kuri’a sun yi tir da yadda shugaban na Amurka ya tunkari annobar coronavirus.

A yayin hirar ta karshen mako, Trump ya bayyana Biden a matsayin mai takaitaccen tunani, yana mai cewa, muddin aka zabi dan adawar nasa a ranar 3 ga watan Nuwamba, to lallai zai ruguza Amurka.

Trump wanda ke fuskantar tarin kalubale kan bazuwar cutar coronavirus da matsalar nuna wariya da kuma tangardar tattalin arziki, ya kara da cewa, Biden, tsohon mataimakin shugaban kasa, zai kara wa Amurkawa kudaden harajin da suke biya da ninki uku, sannan kuma zai katse kudaden tallafin da ake bai wa rundunar ‘yan sandan kasar.

Har ila yau Trump ya ce, addini zai gushe, yana shagube ga ‘ya’yan jam’iyyar Democrat da suka haramta gagarumin taron masu ibada a coci-coci don hana yaduwar coronavirus.

A yayin da aka yi masa tambaya kan ko zai amince da sakamakon zaben mai zuwa muddin ya yi rashin nasara, sai shugaban na Amurka ya bada amsar cewa, zai ga yadda za ta kaya, amma haka kurum dai ba zai ce eeh ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.