EU-Amurka

EU ta yi barazanar lafta wa Amurka haraji kan Airbus

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci Amurka da ta janye harajin da ta lafta mata saboda rikicin tallafawa kamfanin kera jiragen sama na Airbus, yayin da Kungiyar ta EU ta ce, za ta mutunta ka’idojin Hukumar Kasuwanci ta Duniya.

Kamfanin kera jiragen saman Airbus shi ne ummul'haba'isin rikicin kasuwanci tsakanin EU da Amurka
Kamfanin kera jiragen saman Airbus shi ne ummul'haba'isin rikicin kasuwanci tsakanin EU da Amurka REUTERS/Regis Duvignau/File Photo
Talla

Harajin na biliyoyin Dala da Amurkar ta lafta kan kayayyakin kasashen Turai da suka hada da abinci da albarkatun gona da jiragen sama, ya dada tsauri saboda matsalar tattalin arziki da annobar coronavirus ta haddasa.

Kamfanin Airbus ya ce, ya cimma yarjejeniya da gwamnatocin kasashen Faransa da Spain dangane da karin kudin ruwan kudaden da aka bai wa kamfanin domin bunkasa jirginsa samfurin A350 zuwa ga matakin da Hukumar Kasuwanci ta Duniya za ta yi madalla da shi.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce, lura da wannan mataki na cimma yarjejeniya, yanzu haka Amurka ba ta da hurumin sanya haraji kan kayayyakin da kasashen Turai ke fitar da su zuwa ketare karkashin dokokin Hukumar Kasuwanci ta Duniya. Kazalika matakin ya share fagen gaggauta sulhuntawa tsakanin EU da Amurkar.

Kwamishinan Kasuwanci Kungiyar EU, Phil Hogan ya ce, ba za su amince da irin wannan harajin ba kan kayayyakin nahiyar, yana mai cewa, dole ne Amurkar ta soke harajin na rashin adalci , lura da cewa, sun mika wuya ga sharuddan Hukumar Kasuwanci ta Duniya a rikcin kamfanin na Airbus.

Jami’in ya ce, su ma za su dauki matakin ramako muddin Amurkar ta ki janye harajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI