Faransa-Coronavirus

Faransa za ta fara yi wa baki gwajin coronavirus

Wasu jami'an kiwon lafiya da ke yi wa matafiya gwajin cutar coronavirus.
Wasu jami'an kiwon lafiya da ke yi wa matafiya gwajin cutar coronavirus. CLEMENT MAHOUDEAU / AFP

A ziyarar da ya kai wannan Litinin a filin jiragen saman Roissy-Charles-de-Gaulle da ke Paris, firaministan Faransa Jean Castex, ya ce jami’an kiwon lafiya za su gudanar da gwaji kan bakin da ke shiga Faransa daga kasashe 16 da cutar Covid-19 ta tsananta.

Talla

Firaminista Castex, ya ce Faransa ba za ta amince da masu kai ziyara daga wadannan kasashe 16 ba ciki har da Amurka da kuma Brazil lura da yadda wannan annoba ta tsananta a cikinsu.

Sauran kasashen da matakin zai shafa su ne Algeria da Bahrain da Isra’ila da India da Afrika ta Kudu da kuma Kuweti, sai kuma Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da Panama da Peru da Serbia da Turkiya da kuma Madagascar.

Firaminista Castex ya ce, an shirya daukar tsauraran matakai na kiwon lafiya a kan duk wanda zai bar Faransa zuwa wadannan kasashe 16, kazalika za a dauki irin wadannan matakai ga wanda zai shiga Faransa daga can.

Har ila yau firaminista Castex ya gargadi Faransawa da su guji kai ziyara a yankin Catalan da ke arewa maso gabashin Spain, lura da yadda annobar ta coronavirus ta tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.