Libya

Har yanzu Rasha ce ke rarraba makamai a Libya-Amurka

Tun shekarar 2011 Libya ta tsunduma cikin yakin basasa.
Tun shekarar 2011 Libya ta tsunduma cikin yakin basasa. Abdullah DOMA / AFP

Amurka ta ce ta samu sabbin hotunan da ke tabbatar da cewa Rasha na ci gaba da bai wa ‘yan tawaye makamai a kasar Libya.

Talla

A cikin sanarwar da ta fitar a wannan Juma’a, Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ce daga cikin makaman da Rasha ta bai wa ‘yan tawayen, sun hada da bindigogi da tankokin yaki da makamai masu linzami da jiragen yaki, kuma Rasha na bayar da makaman ne ta hannun wani kamfanin sojin haya a Libyar mai suna Wagner Group.

Hotunan, wadanda tauraron dan Adam ya dauka, sun nuna tarin makamai a sansanin sojin hayan da ke garin Syrte a gabashin Tripoli, yayin da wasu hotunan ke nuna wani jirgin dakon kaya mallakin Rasha na sauke jiragen yaki samfurin IL-76, da makamai masu linzami samfurin SA-22 da kuma motocin yaki masu sulke kusa da Benghazi.

Kwamandan Rundunar Sojin Amurka a nahiyar Afrika wato Africom, Manjo Janar Bradford Gering, ya ce hotunan na tabbatar da irin goyon bayan da Rasha ke bai wa Khalifa Haftar a yakin da ake yi a Libya.

Ko a cikin makon da ya gabata Amurka ta zargi Rasha da raba wa ‘yan tawayen Libya makamai, lamarin da ya yi hannun riga da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 19-70, wanda ya hana shigar da makamai a kasar mai fama da yakin basasa tun 2011.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.