Turkiya

Shugaban Turkiya ya jagoranci sallar Juma'a a Hagia Sophia

Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya jagoranci sallar Juma’a a cikin shahararren ginin nan mai dimbin tarihi na Hagia Sophia wanda ya shafe daruruwan shekaru a matsayin Coci kafin a mayar da shi Masallaci.

Shugaban Tayyip Erdogan tare da mukarrabansa a wurin sallar Juma'a a Hagia Sophia
Shugaban Tayyip Erdogan tare da mukarrabansa a wurin sallar Juma'a a Hagia Sophia Reuters
Talla

Al’ummar Musulmi masu tarin yawa ne suka halarci sallar Juma'ar na yau duk da sharuddan nesa nesa da juna da dokar sanya kyallen rufe baki da hanci da aka kafa domin hana bazuwar cutar coronavirus.

Shugaba Erdogan ya halarci sallar ce tare da ministocinsa.

Tun da farko dai, an samar da wannan kasaitaccen gini ne a matsayin Coci a Daular Gabashin Roma, sai dai kuma daga bisani aka mayar da shi Masallaci, wato bayan  Daular Usmaniya ta ci birnin Santanbul a shekarar 1453.

A shekara ta 1935 ne mutumin da ya assasa Turkiya wadda babu ruwanta da addini, Kamal Ataturk , ya mayar da ginin a matsayin wajen adana kayan tarihi.

Ko a yau Juma'a sai da kasar Girka ta soki matakin mayar da ginin Masallaci, yayin da wasu kungiyoyin Kiristoci ka cewa, wannan rana ta zame musu ranar zaman makoki saboda mayar da ginin Cocin Masallaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI