Coronavirus

Wadanda Coronavirus ta kama a duniya sun haura miliyan 16

A yau Lahadi adadin wadanda suka harbu da cutar coronavirus ya zarta miliyan 16, fiye da rabinsu kuma a nahiyar Amurka da yankin Caribean suke, a cewar alkalumman kamfanin dillancin labaran Faransa.

Kwayar cutar Covid 19.
Kwayar cutar Covid 19. NEXU Science Communication/via REUTERS
Talla

Daga cikin wannan adadi da suka kamj da cutar, dubu dari 6 da 45 da dari da 84 ne suka mutu, kuma Amurka ce annobar ta fi yi wa ta’adi, inda mutane miliyan 4 da dubu dari da 78 da 21 suka harbu, dubu dari da 46 da dari 4 da 60 sun ce ga garinku nan.

A Latin Amurka da yankin Caribean, akwai mutane miliyan 4 da dubu dari 3 da dari 9 da 15 da cutar ta kama, dubu dari da 82 da dari 5 da 1 sun mutu, sai kuma nahiyar Turai, inda miliyan 3 da dubu 52 da dari da 8 suka harbu, dubu dari 2 da 7 da dari 7 da 34 sun mutu.

Wannan annoba dai sai ci gaba da yaduwa take, kuma fiye da mutane miliyan biyar ne aka sanar sun harbu da cutar Covid 19 tun da aka shiga watan Yulin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI