Sarki Napoleon na cikin musibun da suka hana aikin hajji
A ranar Laraba ake sa ran fara gudanar da aikin hajjin bana tare mahajjata kimanin dubu 10 kacal bayan mahukuntan Saudiya sun takaita adadin mahajjatan saboda annobar coronavirus.Ba a karon farko kenan ba da ake samun irin wannan tarnaki, domin kuwa tarihi ya nuna cewa, tashe-tashen hankula da musibu sun hana gudanar da aikin hajjin a shekarun baya.
Wallafawa ranar:
Tarihi ya nuna cewa, a shekarar 1798, an soke aikin hajji baki daya bayan Sarki Napoleon na Faransa ya mamaye yankin gabas ta tsakiya, lamarin da ya hana maniyata zuwa Saudiya domin sauke farali.
A karon farko a tarihin baya-bayan, an hana miliyoyin maniyata daga kasashen duniya zuwa Saudiyar saboda annobar coronavirus.
A bangare guda, an samu wasu jerin ibtila’o’i da suka mamaye aikin hajjin, inda a shekarar 2015, turmutsutsi ya yi sanadin mutuwar alhazai dubu 2 da 300, baya ga wata kugiyar gini da ta kashe fiye da mahajjata 100 bayan ta rikito.
A shekarar 2006, an samu wani turmutsutsin da ya kashe mutane 364 a Mina, yayin da ginin wani otel ya rufta tare da kashe mutane 76 duk dai a shekarar.
A shekarar 2004, wani turmutsutsin ya kashe mahajjata 251, inda makamancin wannan ibtila’in ya kashe jumullar mutane 46 a 2003 da 2001.
A 1998, fiye da mutane 118 ne suka mutu saboda turmutsutsin Mina. Sai kuma a shekarar 1997 da wata gobara ta kashe mutane 343.
Haka ma a 1994, wani turmutsutsin ya kashe mahajjata 270, yayin da a 1990, alhazai dubu 1 da 426 suka riga mu gidan gaskiya bayan na’urar bada iska ta karkashin kasa ta daina aiki.
A shekarar 1987, hukumomin Saudiya sun dakatar da wata haramtacciyar zanga-zangar da Iraniyawa suka gudanar, kuma an samu mutane fiye da 400 da suka mutu a wannan tarzoma.
A shekarar 1979, daruruwan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mahajjata a Masallacin Ka’aba, inda daga bisani aka samu asarar rayuka 153, yayin da a 1975, wata gobara ta kashe alhazai 200.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu