Amurka na korar 'yan Afrika duk da rufe kan iyakoki
Amurka ta mayar da ‘yan Afrika kusan 190 zuwa kasashensu na asali duk da dokar takaita tafiye-tafiye don hana bazuwar cutar coronavirus, matakin da masu rajin kare hakkin dan Adam ke kallo a matsayin wariyar launin fata.
Wallafawa ranar:
Amurka ta yi gaban kanta wajen tasa keyar ‘yan Afrika zuwa kasashensu na asali, inda ta yi biris da dokar hana tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa.
Wasu alkaluma da Hukumar Shige da Fice ta Amurka ta fitar sun nuna cewa, daga ranar 1 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Yunin bana, an kori ‘yan Afrika 189 a daidai lokacin da ake tsaka da fama da annobar coronavirus.
Kasashen da Amurkar ta maido musu da mutanensu sun hada da Najeriya da Ghana da Senegal da Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Liberia da kuma Masar.
Wadannan kasashen in ban da Masar duk sun rufe kan iyakokinsu tun bayan barkewar coronavirus a farkon wannan shekara, yayin da Amurkar ke amfani da jiragen haya wajen gwamutsa ‘yan Afrikan don mayar da su nahiyar.
Salon da Amurkar ta yi amfani da shi, shi ne sanya ‘yan Afrikan a cikin jirgin fasinjar kasashe makwabta da ba su rufe iyakokinsu ba, inda daga nan bakin za su kama hanyar garuruwansu.
Kungiyar Kare Hakkin Baki ta Hadin Guiwa tsakanin Kamaru da Amurka, ta yi tur da matakin tasa keyar ‘yan Afrikan, tana mai bayyana haka a matsayin nuna wariyar launin fata.
Matakin mayar da baki ‘yan Afrika gida, ya ta’azzara karkashin mulkin shugaba Donald Trump, inda gwamnatinsa ta takaita shigowar baki daga Najeriya da Tanzania da Sudan da Eritrea da Libya da kuma Somalia, matakin da masu rajin kare hakkin dan adam suka caccaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu