Kasashen duniya sun fara maido da dokokin yaki da coronavirus
Kasashen duniya da dama sun fara maido da dokar takaita zirga-zirga a wannan mako, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar sake bazuwar cutar coronavirus a karo na biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni na cewa, cutar coronavirus ta ta’azzara hatta a kasashen da suka samu nasarar takaita yaduwarta a kwanakin baya.
Australia ta sanar da karuwar mutanen da cutar ke harba a kowacce rana , yayin de Vietnam ke tilasta wa dubban masu yawon bude ido ficewa daga tsakiyar birnin Danang saboda bazuwar cutar, inda a China aka tabbatar cewa, coronavirus na ci gaba da yaduwa tsakanin jama’ar kasar.
Hukumomin Hong Kong kuwa, sun haramta taruwar mutane fiye da biyu a wuri guda, baya ga sake rufe gidajen kalace tare da wajabta amfani da kyallen rufe fuska.
Kazalika wannan cuta ta sake ta’azzara a Spain, kasar da ta taba kasancewa cibiyar annobar covid-19, lamarin da ya sa a yanzu, Birtaniya ta wajebta killace duk wani matafiyi da ya yi balaguro daga kasar har tsawon makwanni biyu.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sake nanata cewa, takaita zirga-zirga kadai, ba za ta rage bazuwar wannan annoba ba, har sai an hada da tsarin nesa nesa da juna da rufe baki da hanci .
Cutar coronavirus ta lakume rayukan mutane fiye da dubu 654, kuma nahiyar Turai ke da kashi daya bisa uku na wannan adadin mamatan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu