Gurbatacciyar iska na barazana ga lafiyar al'ummar duniya - AQLI

Wani bincike ya nuna cewa Gurbataccen iska na barazanar katse rayuwar al’umman duniya da kusan shekaru biyu.

Hayaki mai guba a wani yanki na kasar Ukraine
Hayaki mai guba a wani yanki na kasar Ukraine REUTERS / Gleb Garanich
Talla

Hakan na kunshe cikin rahoton da kungiyar dake rajin tattabar da ingantancen iskar Shaka wato AQLI, ta da fitar Talatan nan, tana mai cewa rashin ingancin iska nadaga cikin "mafi girman hadari ga lafiyar ɗan adam".

AQLI ta ce yayin da kasashen duniya ke rige-rige a kokarinsu na laluben rigakafin shawo kan annobar korona, gurbatatcen iska zai ci gaba haifar da rage rayuwa da rashin lafiya ga biliyoyin mutane a fadin duniya.

Kungiyar tace, gurbataccen iska, masamman hayakin ababen hawa da makamashin girki da sauransu, na mummunan tasari ga lafiyar al’umma maza da mata, yara da manya.

Kwararru a kungiyar sun gano cewar girman gurbatar yanayi a duniya na tsaya chak tsawon shekaru 20 da suka gabata duk da cewa, kasar China da tafi kowa yawan al’umma a duniya ta rage yawan makamashi dake gurbata yanayin, matakin da ke illa ga lafiyar jama’a fiye ma da cutar COVID – 19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI