Saudiya-Hajji

Musulmai dubu 10 ke halartan Hajjin bana

Yau ake saran maniyata aikin Hajjin bana su fara gudanar da ibadar su da fita zuwa Mina daga Makkah, kafin gobe su tashi zuwa Arfa.

Dakin Ka'aba dake birnin Makkah a kasar Saudiya.
Dakin Ka'aba dake birnin Makkah a kasar Saudiya. Saudi Ministry of Media via AP
Talla

Hukumomin Saudi Arabiya sun dauki matakai da dama domin kare maniyatan daga kamuewa da cutar coronavirus wajen kula da lafiyar su da kuma bada tazara wajen ibada.

Sabanin yadda aka saba ganin maniyata sama da miliyan 2 da rabi na aikin Hajjin, a bana mutane 10,000 kacal zasu sauke farali daga cikin mazauna kasar ta Saudiyya da aka zabo.

Kafofin yada labaran Saudiyya sun nuna hotunan ma’aikata na tsaftace wuraren ibadar da magunguna, cikin su harda Dakin Ka'aba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI