Faransa ta share bakin haure daga birnin Paris
Rundunar ‘yan sandan Faransa ta kwashe ‘yan ci-rani kimanin dubu 1 da 500 daga wani sansani da ke yanki arewacin birnin Paris, lura da barazanar da suke fuskanta ta kamuwa da coronavirus.
Wallafawa ranar:
Bayanai na cewa, ‘yan ci-ranin na rayuwa ne cikin wani mummunan yanayi da kuma rashin tsaftaccen ruwan sha a sansanin na Aubervilliers, lamarin da ke dada jefe su cikin hatsarin harbuwa da cutar.
Da jijjifin ranar Laraba ne ‘yan ci-ranin suka fara shiga motocin bas-bas da aka ajiye a sansanin wanda ya cika makil da bakin masu neman zama a nahiyar Turai.
Wata jami’ar Kungiyar Agaji, Silvana Gaeta ta ce, ‘yan ci ranin sun galabaita, tana mai cewa, a karo na goma kenan da ake sauya wa wasu daga cikinsu matsuguni kuma akasarinsu ana jibge su ne a dakunan motsa jiki na dan wani lokaci, yayin da wasu ke ci gaba da gararanba a kan tituna.
Jami’ar Kungiyar Agajin ta Solidarite Migrants Wilson, ta caccaki hukumomin Faransa kan yunkurinsu na jibge ‘yan ci-ranin a boyayyun wurare don mutane su yi zaton cewa, ‘suna cikin yanayi mai kyau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu