Saudiya

Hawan Arafa ya banbanta da na shekarun baya

A wannan Alhamis Mahajjata a Saudiya ke hawan Arafa da ke zama babban rukunin aikin hajji, inda aka tanadi cikakken tsaro duk da cewa tsirarun mutane ke gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus.

Mahajjata a kan dutsen Arafa
Mahajjata a kan dutsen Arafa REUTERS
Talla

A karon farko a tarihin baya-bayan nan, tsirarun mutane ne da adadinsu bai wuce dubu 10 ba ke gudanar da aikin hajjin bana, sabanin shekarun da suka gabata da ake samun kimanin Mahajjata miliyan biyu da doriya.

Mahajjatan na bana sanye da kyallan rufe baki da hanci da kuma nesa nesa da juna, sun isa filin dutsen Arafa a cikin motocin bas-bas daga Mina, yayin da mahukuntan Saudiya suka shinfida sharuddan hana yaduwar cutar coronavirus.

An yi wa Alhazan gwajin zafin jikinsu kafin samun damar isa filin na Arafa domin sauraren huduba da wa’azi daga limami tare da gudanar da jarin addu’o’i da wasu nau’uka na ibadu da suka hada da karatun Al-Qur’ani.

Akwai dai gagarumin banbanci game da yawan mahalarta filin na Arafa a wannan Laraba, idan aka kwatanta da bara, inda dubban Mahajjata suka haye kan dutsen na Arafa.

Kazalika yau din ne Mahajjatan ke wucewa Muzdalifa daga Arafa, inda za su kwana a filin Allah-Ta’ala domin kintsa wa rukunan karshe na aikin hajjin da suka hada da jifan shaidan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI