Coronavirus

Mamatan corona sun haura dubu 660

Yawan mutanen da annobar coronavirus ta halaka a sassan duniya ya haura dubu 660, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura miliyan 16 da dubu 750, bayan shafe watanni 7 da bullar annobar daga China.

Jami'an yaki da cutar coronavirus
Jami'an yaki da cutar coronavirus William WEST / AFP
Talla

Sabbin alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar tun bayan bullar cutar a watan Disambar bara, akalla rayuka dubu 660 da 787 coronavirus ta lakume a duniya, daga cikin miliyan 16 da dubu 789 da 80 da suka kamu, sai dai daga cikinsu, miliyan 9 da dubu 555 da 900 sun warke.

Har yanzu Amurka ke kan gaba a tsakanin kasashen da cutar ta fi yin ta’adi, inda ta halaka sama da mutane dubu 149 da 200, daga cikin mutane kusan miliyan 4 da dubu 400 da suka kamu, yayin da akalla miliyan 1 da dubu 355 da 363 suka warke.

A Brazil mutane dubu 88 da 539 annobar ta COVID-19 ta kashe, a Birtaniya rayuka dubu 45 da 878, sai Mexico da ta rasa akalla mutane dubu 44 da 876.

A nahiyar Afrika, yawan rayukan da cutar ta salwantar a yanzu ya kai akalla dubu 18 da 496 daga cikin mutane dubu 875 da 652 da suka kamu, sai dai fiye da rabinsu sun warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI