WHO-Coronavirus

Cutar Coronavirus za ta dade a doron kasa - WHO

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO. Christopher Black/WHO/Handout via REUTERS

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa za a shafe lokaci mai tsawo ba tare da samun nasarar kawar da annobar coronavirus ba.

Talla

Hukumar ta WHO ta bayyana haka ne, bayan gudanar da taron gaggawa kan halin da ake ciki dangane da yakar annobar, watanni 6 bayan bullarta daga China a disambar shekarar bara.

Zuwa yanzu annobar ta lakume rayukan sama da mutane dubu 680 yayin da yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya haura miliyan 17, sai dai sama da miliyan 10 daga ciki sun warke.

Hukumar lafiya ta duniyar da ta jaddada mahimmancin goyon bayan al’umma a yakin da ake da COVID 19.

WHO ta ce hatsarin annobar ya kai kololuwa, kuma ana iya shafe gomman shekaru ana jin tasirinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI