SpaceX

'Yan saman jannatin Amurka sun dawo duniya

BoB Behnken da Doug Hurley da suka dawo daga duniyar Mars.
BoB Behnken da Doug Hurley da suka dawo daga duniyar Mars. space.com

‘Yan sama jannati biyu da cibiyar harba tauraron dan adam mai zaman kanta ta farko da ke Amurka wato SpaceX ta cilla, sun dawo duniya cikin koshin lafiya bayan wannan tafiya ta tsawon watanni biyu a matsayin gwaji zuwa duniyar Mars.

Talla

‘Yan sama jannatin biyu, Bob Behnken da Doug Hurley sun yi tafiyar kasa da awa daya ne  cikin tauraron dan adam mai suna Dragon da ke gudun kilomita dubu 28 kowace sa’a guda domin dawowa duniyar da muke rayuwa, inda ya sauka a gabar tekun Mexico.

Wannan gagarumin aiki da cibiyar harba tauraron dan adam mai zaman kanta SpaceX ta yi, ya kawo karshen yadda Rasha ta mamaye wannan bagare na tafiye-tafiye zuwa sararin samaniya a cikin shekaru 9 bayan da Amurka ta daina aiki da nata tauraron dan adam tun a shekara ta 2011.

SpaceX, wani attajirin Amurka mai suna Elon Musk ne ya zuba makuden kudadensa domin fara aikin gina wannan cibiya mai zaman kanta irinta ta karo a duniya a shekara ta 2002, kuma shugaba Donald Trump da kansa ya kasance a halarce lokacin da tauraron Dragon ya yi tashin farko zuwa sararin samaniya a cibiyarsa da ke Florida.

Bayan saukarsu a gabar tekun Mexico wadda aka tsara saboda kauce wa duk wata tangarda da za a iya samu saboda matsalar yanayi, ‘yan sama jannatin biyu sun tashi a wani jirgin sama domin komawa cikin iyalansu a birnin Houston.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI