EU

EU ta kaddamar da bincike kan shirin Google na sayen Fitbit kan dala biliyan 2

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai EU, ta kaddamar da bincike kan shirin da kamfanin fasahar sadarwa na Google ke yi na saye kamfanin Fitbit mai kera agogunan hannu amsu amfani da manhajar waya kan dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 100.

Wasu daga cikin na'urorin da kamfanin fasaha na Fitbit ke kerawa
Wasu daga cikin na'urorin da kamfanin fasaha na Fitbit ke kerawa AFP
Talla

Makasudin binciken dai shi ne tantance ko cinikin zai baiwa Google wata damar da ta zarce ka’ida wajen tserewa sauran kamfanoni takwarorinsa.

A watan Nuwamban shekarar bara, kamfanin Google ya sanar da cimma yarjejeniyar saye kamfanin Fitbit dake kera agoguna masu dauke da na’urorin aiki kai tsaye da manhajojin tantance lafiyar jikin dan adam.

Sai dai shi kansa kamfanin na Google yana kera manhajojin da agogunan zamani masu dauke fasahar tantance lafiyar jiki ke amfani da su, abinda ya sanya kungiyar kasashen Turai, bayyana damuwa kan cewar kamfanin na Google zai samu damar da ta zarce ka’ida a kasuwar fasahar sadarwa, wajen fin karfin sauran kamfanoni takwarorinsa, muddin ya mallaki rumbun fasahohin kamfanin Fitbit.

A halin yanzu hukumar gudanarwar kungiyar kasashen Turan EU na da wa’adin watanni 3, na gudanar da binciken tantance katafaren cinikin da Google ke shirin yi, wanda bayan kammala shi za ta tantance yiwuwar gindayawa kamfanin wasu ka’idoji don baiwa abokan hamayyarsa a kasuwar fasahar sadarwa kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI