Coronavirus

An fara gwajin riga-kafin corona a China

Masu binciken kimiya a dakin gwaje-gwaje da ke China.
Masu binciken kimiya a dakin gwaje-gwaje da ke China. NOEL CELIS / AFP

An soma gwajin riga-kafin cutar coronavirus kan mutane a China, wanda kamfanonin sarrafa magunguna na Jamus BioNTech da kuma na Fosun Pharma da ke kasar ta China suka samar.

Talla

Cikin sanarwar da suka fitar, kamfanonin na BioNTech da Fosun sun ce tuni aka aiwatar da gwajin maganin riga-kafin na BNT162b1 kan mutane 72.

Kwararru za su aiwatar da kashin farko na gwajin riga-kafin cutar ta coronavirus ne kan jumullar mutane 144 a China, kuma za a soma ne da mutane masu shekaru 18 zuwa 55, kafin tsofaffi su biyo baya, wadanda za su shafe kwanaki 21 suna karbar maganin gwajin karkashin kulawar tawagar masanan.

Yanzu haka manyan kamfanonin harhada magunguna, da kuma cibiyoyin kimiyya a sassan duniya, sun dukufa wajen bincike kan magungunan riga-kafin cutar coronavirus daban daban sama da 200, don gaggauta kawo karshen annobar da kawo yanzu ta halaka sama da mutane dubu 700 a sassan duniya.

Sai dai mai yiwuwa magungunan Rashar da China za su fuskanci turjiya daga wasu kasashen Turai, musamman Amurka wadda ta fito fili ta nuna rashin gamsuwa da matakan da ake bi wajen tantance ingancin magungunan.

A ranar Laraba Amurka ta rattaba hannu kan yarjejeniyar biyan kamfanin Johnson & Johnson Dala biliyan 100 domin samar da riga-kafin cutar coronavirus da sharadin cewar kamfanin zai bai wa Amurka adadin sunkin maganin miliyan 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.