Lebanon

Macron na ziyarar jaje a Lebanon

Shugaban Faransa Emmanuel Macron,
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, AP Photo / Olivier Matthys, Piscine

A wannan Alhamis shugaban Faransa Emmanuel Macron ke ziyara a  Lebanon bayan kasar ta gamu da mummunan ibtila'in da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 100 sakamakon fashewar sinadarai a tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut.

Talla

Shugaba Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai ziyarci Beirut ne don isar da sakon ‘yan uwantaka da goyon baya ga al’ummar Lebanon.

Da sanyin safiyar wannan Alhamis ne shugaba Macron ya kama hanyar Beirut da ya gamu da ibtila'in.

A ranar Talata da ta gabata ne wani abin da ake zargin sinadarin ammonium nitrate da ba a adana ta hanyar da ta dace ba ne ya yi bindiga a tashar jiragen ruwan Beirut, lamarin da ya girgiza mazauna gidajen da ke makwabtaka da tashar, yayin da akalla mutane dubu 300 suka rasa muhallansu.

Fadar shugaban Faransa ta Elysee ta ce shugaba Macron zai gana da illahirin masu ruwa da tsaki a siyasar Lebanon da suka hada da shugaba Michel Aoun da Firaminista Hassan Diab.

Dukkannin bangarorin za su yi fatar ziyarar ta haifar da da-mai-ido, akasin wacce Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya kai a watan da ya gabata.

Wannan ce matsala ta baya bayan nan da kasar da ke fama da rikicin siyasa da matsin tattalin arziki irin wadda ba ta taba fuskanta ba ta tsinci kanta a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI